logo

HAUSA

Syria ta shiga shawarar Sin ta ziri daya da hanya daya

2022-01-13 10:47:28 CRI

Syria ta shiga shawarar Sin ta ziri daya da hanya daya_fororder_220113-Saminu2-SyriaBelt & Road

A jiya Laraba ne kasar Syria ko Sham, ta bayyana amincewar ta, ta shiga shawarar Sin ta ziri daya da hanya daya ko BRI a takaice, matakin da mahukuntan kasar suka ce zai taimaka, wajen budewa Syriar damar fadada damammaki, da hadin gwiwar ta da Sin, da ma sauran wasu kasashe.

An gudanar da bikin shigar Sham shawarar BRI ne jiya Laraba, a harabar hukumar tsare tsare da hadin gwiwar kasa da kasa, kuma bikin ya samu halartar shugaban hukumar Fadi Khalil, da jakadan Sin a kasar Feng Biao. Sassan biyu sun kuma yi amfani da wannan dama wajen sanya hannu kan takardar fahimtar juna, mai nasaba da shigar Syriar wannan shawara ta BRI.

Da yake tsokaci kan hakan, Fadi Khalil, ya ce ta hanyar rungumar shawarar ziri daya da hanya daya, Sham ta farfado da rawar da ta taka, a tsohuwar hanyar siliki, kuma hakan zai taimaka mata, wajen bunkasa hadin gwiwa da Sin, da ma sauran sassan kasa da kasa dake fatan kulla kawance da ita.

A nasa bangare kuwa, Feng ya ce hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, zai samar da babbar gudummawa, ga sake tsara harkokin tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’ummar Syria, kana zai hade bangaren shawarar ziri daya da hanya daya, da shawarar neman ci gaba ta Sham. (Saminu Fagam)