logo

HAUSA

Kwararru: Dokar kasar Amurka game da ‘yan kabilar Uygur ba ta da adalci

2022-01-13 21:28:04 CMG

Kwararru: Dokar kasar Amurka game da ‘yan kabilar Uygur ba ta da adalci_fororder_220113-Xinjiang-Bello

A yau Alhamis, gwamnatin jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kira wani taron manema labaru, inda wasu kwararru daga kasashe daban daban, suka yi tsokaci kan dokar da kasar Amurka ta tsara, ta hana tilastawa ‘yan kabilar Uygur aiki, inda suka ce babu adalci a cikin wannan doka, kana maganar tilasta aiki sam ba ta da tushe.

Hiroshi Onishi, farfesa daga kasar Japan, wanda ya taba gudanar da nazari a Kashgar na jihar Xinjiang, kan yadda ake samar da aikin yi a wurin. A cewarsa, bincike ya nuna cewa, an kaurar da wasu mutane daga Xinjiang zuwa wasu yankuna masu ci gaban tattalin arziki dake bakin teku, kuma an yi haka ba domin tilasta musu aiki ba ne. Maimakon haka, ana neman samar musu da guraben ayyuka masu kyau, ta yadda za su samu damar kyautata zaman rayuwarsu.

A nashi bangare, Alim Satar, wani masanin ilimin shari’a dake aiki a jami’ar Xinjiang ta kasar Sin, ya ce, ma’anar kalmar “tilastawa wani aiki” ita ce sanya mutum aiki ba da son ransa ba, kana idan ya ki yin aiki, za a yi masa hukunci. Amma abun da ake yi a jihar Xinjiang ba haka ba ne. Wato kasar Amurka na neman yin amfani da kalmar “tilasta aiki” don siffanta dabarar samar da aikin yi a jihar Xinjiang, sai dai wannan batu ya sabawa ainihin abun da yake faruwa. (Bello Wang)

Bello