logo

HAUSA

Adadin ‘yancin mallakar fasahar zamani ya karu a kasar Sin

2022-01-13 10:23:41 CRI

Adadin ‘yancin mallakar fasahar zamani ya karu a kasar Sin_fororder_专利

A halin yanzu, kasar Sin tana samun ci gaba mai inganci, don haka ‘yancin mallakar fasaha yana kara taka rawa ga kirkire-kirkire, da kyautata tsarin kasuwanni da kuma bude kofa ga ketare.

Sabbin alkaluman hukumar kula da ‘yancin mallakar fasaha ta kasar Sin sun nuna cewa, a shekarar 2021 ta gabata, adadin ‘yancin mallakar fasaha a fannonin fasahohin zamani na kasar ya karu a kai a kai, yayin da karfin kirkire-kirkiren kasuwannin kasar ke kara karfafuwa.

Ya zuwa karshen bara, adadin ‘yancin mallakar fasaha na kamfanonin kasar Sin ya kai miliyan 1 da dubu 908, adadin da ya karu da kaso 22.6 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2020. A cikin adadin, ‘yancin mallakar fasaha na kamfanonin fasahohin zamani ya kai miliyan 1 da dubu 213, lamarin da ya nuna cewa, karfin kirkire-kirkiren kasuwannin kasar Sin yana kara karfafuwa.

Yayin taron ganawa da manema labaran da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira jiya, kakakin watsa labarai na hukumar kula da ‘yancin mallakar fasaha ta kasar Hu Wenhui, ya bayyana cewa,“Bisa kididdigar da aka yi kan fannonin fasaha 35 da hukumar ‘yancin mallakar fasaha ta duniya ta tsara, ya zuwa karshen shekarar 2021, fannonin fasaha uku, wadanda suka fi saurin ci gaba a kasar Sin, sun hada da dabarun sarrafa fasahar sadarwa, da fasahar kwanfuta, da kuma fasahar kiwon lafiya, lamarin da ya nuna cewa, ‘yancin mallakar fasaha yana sa kaimi, ga ci gaban sana’o’i, da kuma kyautata rayuwa da lafiyar al’ummun kasar.”(Jamila)