logo

HAUSA

Kasashe 8 sun rasa damar su ta kada kuri’a a MDD

2022-01-13 10:53:59 CRI

Kasashe 8 sun rasa damar su ta kada kuri’a a MDD_fororder_220113-Saminu1-UN

Kasashen Iran da Venezuela na cikin kasashe 8 da suka rasa damar su ta kada kuri’a a zauren MDD, bayan da suka gaza ba da gudummawar su ta kudaden gudanarwar majalissar kamar yadda doka ta tanada. Sauran kasashen su ne Sudan, da Antigua da Barbuda, da Congo, da Guinea, da Papua New Guinea da kuma Vanuatu.

Da yake tsokaci kan hakan, Paulina Kubiak, kakakin shugaban zaman majalissar na 76, ya ce cikin wata wasikar da babban magatakardar MDDr Antonio Guterres ya aikewa majalissar, ya fayyace cewa, doka ta 19 ta tanaji haramtawa mambobi kada kuri’un su a zauren, muddin suka kasa ba da adadin da ya kai, ko ya dara abun da ya dace su bayar a shekaru 2.

Antonio Guterres ya ce, mambobin MDDr na iya samun rangwame kan wannan hukunci ne kawai, idan sun iya nuna cikakkiyar shaidar cewa ba su da halin biyan kudaden, kamar yadda a shekarar nan ta 2022, hakan ta faru ga tsibirin Comoro, da Sao Tome da Principe, da Somalia.Yanzu haka dai Iran na da bukatar baiwa MDDr a kalla kudin da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 18.4, yayin da Venezuela za ta ba da a kalla dalar Amurka miliyan 39.8, kafin su sake samun damar kada kuri’un su. (Saminu Hassan)