logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya godewa Sin bisa karin gudunmawar alluran riga-kafin COVID-19 miliyan 10

2022-01-13 10:18:39 CRI

Shugaban Zimbabwe ya godewa Sin bisa karin gudunmawar alluran riga-kafin COVID-19 miliyan 10_fororder_220113-Ahmad2-Zimbabwe

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya yabawa gwamnatin kasar Sin bisa gudunmawar da ta baiwa kasar na karin alluran riga-kafin annobar COVID-19 guda miliyan 10.

Mnangagwa ya ce, kasar Zimbabwe za ta karbi riga-kafin na kamfanin Sinovac guda miliyan 6, da kuma na kamafanin Sinopharm guda miliyan 4, wadanda za su yi matukar taimakawa kasar wajen saukaka mata kalubalolin fannin lafiya.

Gudunmawar kari ne kan allurai miliyan 2 da kasar Sin ta baiwa kasar Zimbabwe tun daga watan Fabrairun shekarar 2021.

Ya ce, gwamnati tana matukar godiya ga tallafin da kasar Sin take baiwa kasarsa da kuma kokarin da Sin ke yi wajen tabbatar da samun wadatar riga-kafin mai inganci ba kawai ga kasar Zimbabwe da nahiyar Afrika ba, har ma da dukkan kasashen duniya.

Kasar Zimbabwe tana ci gaba da sa kaimi don tabbatar da ganin an yi karin mutanen kasar riga-kafin annobar COVID-19, ya zuwa ranar Talata, mutanen Zimbabwe 3,197,072 sun karbi cikakkun riga-kafin zagaye na biyu, yayin da mutane 4,176,397 sun karbi zagayen farko na riga-kafin, kana wasu mutanen kasar 15,185 sun karbi riga-kafin mai kara karfin garkuwar jiki. (Ahmad)