logo

HAUSA

Pierre Ducrey ya jinjinawa tsarin gudanarwar gasar Olympics na birnin Beijing

2022-01-13 11:24:22 CRI

Pierre Ducrey ya jinjinawa tsarin gudanarwar gasar Olympics na birnin Beijing_fororder_220113-Saminu3-Olympics

Daraktan tsare tsare na kwamitin shirya gasar Olympic ta kasa da kasa Pierre Ducrey, ya shaidawa mahalarta taron masu ruwa da tsaki ta kafar bidiyo, game da gasar Olympics ta birnin Beijing dake tafe cewa, ya gamsu da cikakken tsarin amfani da na’urorin zamani, domin ba da kariya ga mahalarta gasar.

Pierre Ducrey, ya ce a tsawon mako guda, tun bayan isowarsa birnin Beijing, ya lura da ayyukan gwajin da ake gudanarwa, a wuraren gudanar da wasanni, da kauyen wasanni da sauran su, don haka ko shakka babu gasar dake tafe za ta gudana cikin nasara.

Ducrey, ya kuma jinjinawa salon amfani da na’urorin zamani da aka tanada domin wannan babbar gasa, wadda ya ce za ta gudana cikin yanayi na tsaron lafiya, duba da yadda aka tsara daukar matakan yaki da cutar COVID-19 daki daki, cikin kundin gasar da tuni aka rarraba.

Jami’in ya ce gwajin COVID-19 na rana ran da za a rika yiwa masu shigowa, da masu fita daga yankunan gudanar gasar, da amfani da marufin baki da hanci na musamman da aka tanada, za su taimaka wajen tabbatar da tsaron lafiyar mahalarta wannan gasa.  (Saminu)