logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya yaba kuzarin da ’yan wasan Super Eagles suka nuna a wasan farko na AFCON

2022-01-13 10:33:12 CRI

Shugaban Najeriya ya yaba kuzarin da ’yan wasan Super Eagles suka nuna a wasan farko na AFCON_fororder_220113-Ahmad1-AFCON

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yabawa ’yan wasan Super Eagles, babbar kungiyar wasan kwallon kafan Najeriya, bisa  bajintar da suka nuna a wasansu na farko na neman cin kofin kasashen Afrika karo na 33 AFCON wanda ke gudana a kasar Kamaru.

Kungiyar kwallon kafan Super Eagles ta doke takwararta ta kasar Masar da ci 1-0 a wasan farko na rukunin D wanda aka fafata a birnin Garoua a ranar Talata.

A wata sanarwa, shugaba Buhari ya ce, ya yi amanna cewa irin bajintar da ’yan wasan Super Eagles suka nuna misali ne na abin da ake tsammani daga kungiyar wasansu dake tafe a nan gaba inda ake fatan za su yi zarra a sauran wasannin da za ta fatata da sauran takwarorinsu.

Shugaban Najeriyar ya baiwa babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar tabbacin goyon bayansa, inda ya bukaci kungiyar dake karkashin jagorancin Augustine Eguavoen kana mai horar da ’yan wasan, da su mai da hankali kan wasanninsu, kuma su kasance jakadu na gari a filin wasan da wajen filin, kana su yi kokarin taka leda a wasanninsu don faranta ran dunbun magoya bayansu da dukkan ’yan Najeriya. (Ahmad Fagam)