logo

HAUSA

Kasar Sin tana maraba da kafofin watsa labarai daga dukkan kasashen da za su watsa rahotannin wasannin Olympics na lokacin sanyi

2022-01-13 20:10:19 CMG

Kasar Sin tana maraba da kafofin watsa labarai daga dukkan kasashen da za su watsa rahotannin wasannin Olympics na lokacin sanyi_fororder_220113-media-Olympics-Ibrahim

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana Alhamis din nan cewa, kasarsa tana maraba da kafofin watsa labaru daga dukkan kasashen duniya, da za su watsa rahotanni game da wasannin Olympics na lokacin sanyi, kuma kamar yadda aka saba, za a kare hakki da moriyarsu, da kuma saukaka yadda za su rika ba da rahotannin gasar.

Wang Wenbin ya shaidawa taron manema labarai cewa, kasar Sin tana karfafa gwiwar 'yan jaridun, da su ba da shawarwari masu ma'ana, amma kuma kasar Sin tana adawa da watsa labarai da bayanan karya bisa uzurin 'yancin 'yan jarida na bata sunan kasar Sin da kuma wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing.

Rahotani na cewa, yanzu haka kimanin 'yan jarida da masu daukar hoto 2,500 ne suka gabatar da takundun neman iznin watsa rahotonnin wasannin.(Ibrahim)

Ibrahim