logo

HAUSA

Sabbin layukan samar da wutar lantarki na kasar Sin guda biyu sun sake kafa tarihin tsayin layukan lantarki a duniya

2022-01-13 20:21:21 CMG

Sabbin layukan samar da wutar lantarki na kasar Sin guda biyu sun sake kafa tarihin tsayin layukan lantarki a duniya_fororder_1

An gina wasu manyan hasumiyoyin samar da wutar lantarki guda biyu a lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, lamarin da ya kara kafa wani bajinta a fannin tsayin layukan samar da wutar lantarki a duniya.

Manyan turakan biyu da aka gina a kowane gefe na kogin Yangtze, kogin dake zama mafi tsawo a kasar Sin dake yankin na Jiangsu, sun kai tsayin mita 385, kuma sun karya tarihin tsayin mita 380 da aka kafa, na turken samar da layin wutar lantarki da aka gina a lardin Zhejiang dake makwabtaka da kasar a shekarar 2018.

Tagwayen hasumiyoyin na Jiangsu, sun kai nisan kilomita 2.6, inda suka karfafa layin wutar lantarki a birnin Taizhou da ke arewacin gabar kogin Yangtze da Wuxi ta kudu. Ana kuma sa ran aikin, zai tura wutar lantarki da ya kai kilowatt biliyan 28.9 daga arewacin kogin Yangtze zuwa kudanci a duk shekara, wanda zai iya samar da wutar lantarki ga gidaje miliyan 8.(Ibrahim)

Ibrahim