logo

HAUSA

Mali tana maraba da kasar Sin na karbar bakuncin wasannin Olympic na lokacin hunturu na 2022

2022-01-13 11:07:44 CRI

Mali tana maraba da kasar Sin na karbar bakuncin wasannin Olympic na lokacin hunturu na 2022_fororder_220113-Ahamd3-Mali

Kasar Mali tana maraba da kasar Sin na karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na 2022, kakakin gwamnatin rikon kwaryar kasar, Abdoulaye Maiga ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Maiga ya ce, za a gudanar da gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi karo na 24 a daidai lokacin da ake fama da kalubalen kiwon lafiya sakamakon barkewar annobar COVID-19. Sai dai duk da irin yanayin da ake ciki, wasannin za su ci gaba da kiyaye ruhinsu na karfafa zumunta da alaka a tsakanin kasashen duniya wanda ya yi daidai da manufar ruhin Olympic wanda bai taba bude wata kafa ta siyasantar da harkar wasannin ba.

Za a gudanar da gasar ta Beijing 2022 Olympic ne tsakanin ranar 4 zuwa 20 ga watan Fabrairu. (Ahmad Fagam)