logo

HAUSA

Bankin duniya ya rage mizanin hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya na bana

2022-01-12 10:50:18 CRI

Bankin duniya ya rage mizanin hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya na bana_fororder_20220112-World Bank-Saminu1

Bankin duniya ya rage mizanin hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya da ya yi a baya da kaso 0.2, inda hasashen sa na shekarar bana, ya tsaya kan karuwar kaso 4.1 bisa dari.

Wani rahoto da bankin duniyar ya fitar a jiya Talata, mai kunshe da hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya na shekarar 2022, ya alakanta koma bayan farfadowar tattalin arzikin duniya, da kara bazuwar cutar COVID-19 a sassan duniya, da gurguncewar manufofin ba da tallafi, da tabarbarewar tsarin samar da hajoji.

Rahoton ya kara da cewa, baya ga bullar sabbin nau’o’in cutar COVID-19, akwai kuma kalubale na rashin tabbas game da hauhawar farashin kayayyaki, da matsin tattalin arziki mai nasaba da tarin bashi da ya yiwa kasashe katutu.

Kaza lika, rahoton ya bayyana rashin daidaito da kalubalen tsaro, a matsayin matsalolin dake ciwa kasashe masu tasowa tuwo a kwarya, don haka ba wata hanyar da ta dace, ta mayar da kasashen duniya kan hanyar samun ci gaba, sama da hadin gwiwar kasa da kasa, wajen aiwatar da cikakkun tsare tsare na tunkarar kalubale a matakan kasashe.  (Saminu)