logo

HAUSA

CPI Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 1.5 A Watan Disamba

2022-01-12 19:57:34 CRI

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayyana yau Laraba cewa, kididdigar farashin kayayyakin masarufi ta kasar, wani babban ma'aunin hauhawar farashin kayayyaki, ya karu da kashi 1.5 bisa dari a watan Disamba, wanda ya ragu kadan bisa kashi 2.3 bisa dari na watan Nuwamba .

Alkaluman CPI a shekarar 2021 ya karu da kashi 0.9 cikin dari, wanda ya yi kasa da mizanin da kasar ke fatan samu a shekara da kusan kashi 3 cikin dari. Alkaluman na CPI ya kai kashi 2.5 da kashi 2.9 a shekarar 2020 da ta 2019, bi da bi.

A bisa ga bayanan hauhawar farashin kayayyaki a watan Disamba, farashin kayan abinci ya ragu da kashi 1.2 bisa dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, lamarin da ya sauya karuwar kashi 1.6 cikin 100 a watan Nuwamba. Haka kuma farashin da ba na kayan abinci ba, ya karu da kashi 2.1 cikin dari daga shekarar da ta gabata, inda aka samu sauki daga kashi 2.5 cikin dari a watan Nuwamba.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya