logo

HAUSA

MDD ta fidda dala biliyan 1.9 don taimakawa mutane miliyan 10.9 a Sudan

2022-01-12 11:32:07 CRI

MDD ta fidda dala biliyan 1.9 don taimakawa mutane miliyan 10.9 a Sudan_fororder_20220112-Sudan-Ahmad3

Ofishin kula da ayyukan jinkai na MDD (OCHA), a ranar Talata ya fidda kudi dala biliyan 1.9 domin aiwatar da ayyukan jinkai a kasar Sudan a shekarar 2022.

A cewar ofishin, sama da dala miliyan 800 za a kashe wajen gudanar da ayyukan ceto rayukan al’umma, inda ake sa ran taimakawa mutane marasa galihu kimanin miliyan 10.9 daga cikin adadin mutane miliyan 14.3 dake bukatar agaji a fadin kasar ta Sudan.

Shirin ya kunshi bangarorin tallafi daban daban da suka hada da muhimman hidimomin ayyukan kiwon lafiya, da aikin kandagarki da dakile cutukan da ake dauka ta hanyar ruwan sha da kawar da kwayoyin cutuka masu yaduwa, da samar da ilmi, da kyautata yanayin zaman rayuwa, da samar da ruwa da muhalli mai tsafta.

OCHA ya bayyana cewa, karuwar girman matsalolin da kuma halin kuncin rayuwar da mutane marasa galihu suke fuskanta na bukatar daukin gaggawa da samar da kudaden ayyukan jinkai a kan lokaci. (Ahmad Fagam)