logo

HAUSA

An bukaci abokan huldar Mali su taimaka wajen kafa tubalin zaman lafiya mai dorewa a kasar

2022-01-12 11:06:20 CRI

An bukaci abokan huldar Mali su taimaka wajen kafa tubalin zaman lafiya mai dorewa a kasar_fororder_20220112-Mali-Ahmad1

Wakilin MDD ya bukaci abokan huldar kasar Mali su taimaka wajen kafa tubalin wanzar da zaman lafiya mai dorewa a kasar ta yammacin Afrika mai fama da rikici, El-Ghassim Wane, wakilin musamman na babban sakataren MDD, ya bayyanawa taron kwamitin sulhun MDDr kan batun yanayin rikicin kasar Mali.

Shekaru goma tun bayan barkewar yakin basasar Mali, an yi fatan dakile tashin hankalin tun a farkon barkewarsa sai dai haka ba ta cimma ruwa ba.

A bisa kiyasi, sama da mutane miliyan 1.8 ne ake hasashen za su bukaci tallafin abinci a shekarar 2022 idan an kwatanta da adadin mutane miliyan 1.3 a shekarar 2021, kuma shi ne adadi mafi yawa da aka samu na masu fama da matsalar rashin abinci tun a shekarar 2014.

Duk da wandannan kalubaloli, Wane ya bayyana cewa, yanayin zai iya ta’azzara fiye da halin da ake ciki ba don an samu shigowar al’ummun kasa da kasa ba, da suka hada tura dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na MDD, MINUSMA a shekarar 2013.

Gwamnatin Mali tana ta kokarin lalibo hanyoyin farfado da zaman lafiya bayan jerin koma bayan da aka sha fuskanta tun daga farkon shekarar 2012, da suka hada da juyin mulkin sojojin da bai yi nasara ba, da sake barkewar rikicin mayakan ’yan tawayen Tuareg, da kuma kwace ikon arewacin kasar da ’yan ta’adda da masu tsattsauran ra’ayi suka yi. (Ahmad Fagam)