logo

HAUSA

Xi Ya Jaddada Kyakkyawar Fahimta Da Amfani Da Gogewar Tarihin JKS Na Shekaru Dari

2022-01-11 20:42:24 CRI

Yau ne, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya yi kira da a yi kokarin zurfafa nazari, bita, ba da ilmi da yayata tarihin JKS, ta yadda za a kara fahimta da yin amfani da gogewar tarihin Jam'iyyar a cikin shekaru 100 da suka gabata.

Xi, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude taron nazari da aka shirya a makarantar kwmitin kolin JKS, wanda ya samu halartar jami'an larduna da ministocin gwamnatin kasar.

Xi ya yi nuni da cewa, manufar zaman nazarin ita ce ci gaba da koyo da fahimtar kudurin da aka cimma a cikakken zaman taro karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19.

Ya kuma bukaci kara zaburar da babban ruhin kafuwar jam'iyyar, da sa kaimi ga tarihi, da yin hadin kai, da habaka ruhin gwagwarmaya, da zaburar da 'yayan jam'iyyar baki, da daukacin Sinawa na dukkan kabilu, da su yi aiki tukuru don cimma burin kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, bin tsarin demokuradiyya, wayin kai da jituwa nan da shekarar 2049 wato yayin da za a cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin. (Ibrahim Yaya)

Ibrahim Yaya