logo

HAUSA

Kasar Sin za ta gaggauta aiwatar da muhimman ayyukan shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 14

2022-01-11 09:51:51 CRI

Kasar Sin za ta gaggauta aiwatar da muhimman ayyukan shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 14_fororder_220111-Li Keqiang-Faeza2

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta ce, kasar za ta fadada zuba jari domin gaggauta aiwatar da muhimman ayyukan dake kunshe cikin shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 14, wato tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025.

Taron majalisar da ya gudana jiya Litinin, karkashin Firaministan kasar Sin, Li Keqiang, ya bayyana cewa, bisa la’akari da ingantattun dabaru da kuma shirin da aka yi, ya kamata hukumomi masu ruwa da tsaki su gaggauta gudanar da muhimman ayyukan ta hanyar daukar matakai masu karfi kuma bisa tsari.

A cewar taron, yayin da tattalin arzikin kasar ke kan muhimmiyar gaba, ya kamata kasar ta bada fifiko ga daidaita ci gaban tattalin arziki da ci gaba da aiwatar da dabarun fadada kasuwar cikin gida da daukar matakan bunkasa amfani da kayayyaki da zuba jari.

Kana bisa la’akari da bukatar gaggauta aiwatar da muhimman ayyukan shirin raya kasa karo na 14, kasar za ta tabbatar da samar da kudi da filaye da makamashi ga bangarorin kamar na tabbatar da wadatar abinci da makamashi da manyan masana’antu da kamfanonin fasaha da na jigilar kayayyaki da sadarwa. Baya ga haka, gwamnatocin birane za su saukaka samar da gidaje. (Fa’iza Mustapha)