logo

HAUSA

Gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing za ta sa kaimi ga mu'amalar al'adu da hadin gwiwa

2022-01-11 11:11:19 cri

An gudanar da taron musayar al'adu da fahimtar juna karo na 2, wanda kungiyar musaya ta kasa da kasa ta kasar Sin ta shirya, karkashin sashen kula da harkokin tuntubar kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Mutane kusan 260 daga sassa daban-daban na cikin gida da waje ne suka halarci taron da aka yi jiya Litinin ta kafar bidiyo da kuma ido da ido. Gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ke tafe a nan birnin Beijing, ya zama batun da mahalarta taron suka dora muhimmanci a kai. Dukkansu kuma na cike da kwarin gwiwa kan nasarar da za a samu a gasar, suna masu cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, za ta sa kaimi ga mu'amalar al'adu da hadin gwiwa.

Gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing za ta sa kaimi ga mu'amalar al'adu da hadin gwiwa_fororder_Marbury

A yayin bikin bude taron, Stephon Marbury, babban kocin kungiyar kwallon kwando ta maza ta Beijing, ya bayyana a cikin wani jawabi ta bidiyo cewa, ya kasance mai cin gajiyar mu'amalar al'adu. A cewarsa, ya yi aiki tare da zama a kasar Sin fiye da shekaru 10, kana yana aiki kafada da kafada da takwarorinsa da abokan aikinsa, da jin dadin rayuwa da abokai da masu sha’awar kwallon kwando. Ya ce, yana son zama tare da talakawan kasar Sin, da kuma cin gajiyar albarkar da aka samu a mu'amalar al'adu tsakanin Sin da Amurka.

Gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing za ta sa kaimi ga mu'amalar al'adu da hadin gwiwa_fororder_Masar

A nasa bangaren, Mohamed Elbadri, jakadan kasar Masar a kasar Sin da ya halarci taron, ya bayyana a cikin wata hira da manema labarai cewa, kasar Sin ta yi kokari matuka, wajen shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta birnin Beijing a yayin da ake yakar annobar COVID-19, inda ya yi imanin cewa, kasar Sin za ta samu nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ba a taba yin irinta ba. (Bilkisu Xin)