logo

HAUSA

Gwamnatin Mali ta bayyana takunkuman ECOWAS a matsayi na rashin tausayi

2022-01-11 09:39:38 CRI

Gwamnatin Mali ta bayyana takunkuman ECOWAS a matsayi na rashin tausayi_fororder_220111-Mali government-Faeza1

Gwamnatin Mali ta ce tana da ikon mayar da martani kan takunkuman ECOWAS da ta kira da abun takaici.

Kakakin gwamnatin Mali Abdoulaye Maiga, ya sanar ta gidan talabijin na kasar cewa, kasar ta yanke shawarar kiran dukkan jakadunta dake kasashe mambobin ECOWAS, haka zalika za ta rufe iyakokinta na sama da kasa da kasashen, a wani mataki na mayar da martani.

A cewarsa, gwamnatin na takaicin wadannan matakai na rashin tausayi da za su yi mummunan tasiri a kan jama’ar da dama ke fuskantar matsalolin lafiya da tsaro, musamman ma annobar COVID-19. Ya kuma lashi takobin Mali za ta mayar da martani kan matakan da ya ce sun sabawa doka, da kungiyar ECOWAS mai raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ta sanar ranar Lahadi, bayan kammala taron shugabanninta a birnin Accran Ghana. (Fa’iza Mustapha)