logo

HAUSA

Wang Yi ya amsa tambayoyi bayan kammala ziyara a kasashen Afirka 3

2022-01-11 09:39:42 CRI

Wang Yi ya amsa tambayoyi bayan kammala ziyara a kasashen Afirka 3_fororder_王毅-2

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce duk da yanayi da ake ciki na yaki da annobar COVID-19, ya yi nasarar kammala ziyarar aiki a kasashen Afirka 3, wanda hakan ya tabbatar da dadaddiyar al’adar nan ta ziyarar da duk wani ministan wajen Sin kan kai nahiyar cikin gwamman shekaru.

Wang Yi, wanda ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya Litinin, bayan kammala ziyara a kasashen Kenya da Eritrea da Comoros, ya ce yayin da ya isa Kenya, ya bayyana matsayar kasar Sin ta mara baya, ga manufofin samar da ci gaba cikin lumana a kasar dake kahon Afirka.

Ya ce babban burin Sin shi ne tallafawa kasashen yankin, wajen kaucewa mummunan tasirin takarar manyan kasashen duniya, tare da tabbatar da cewa, suna gudanar da harkokin su ba tare da tsoma bakin wasu daga ketare ba.

Game da zargin da ake yiwa Sin, na danawa kasashen Afirka tarkon bashi kuwa, Wang ya ce Sin da nahiyar Afirka na gudanar da hadin gwiwa yadda ya kamata, an kuma kirkiri batun tarkon bashi ne domin jefa kasashen nahiyar cikin shakku, ta yadda za su dawwama cikin talauci da koma baya.

Don haka a cewar sa, Sin za ta ci gaba da aiki tare da kasashen Afirka, wajen zartas da manufofin inganta rayuwar al’umma, tare da ba da karin gudummawa ga sashen bunkasawa, da zamanantar da masana’antun nahiyar. (Saminu)