logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Kasar Sin Kawa Ce Ta Gaskiya

2022-01-11 14:09:13 cri

Masanin Najeriya: Kasar Sin Kawa Ce Ta Gaskiya_fororder_Sin da Afirka

Shehu malami Michael Ehizuelen, darektan cibiyar nazarin Najeriya a kwalejin nazarin Afirka na jami'ar horar da malamai ta Zhejiang, ya bayyana a baya-bayan nan cewa, duk da barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, har yanzu ya zabi kasashen Afirka domin ziyararsa ta farko a cikin sabuwar shekara, hakan ya sake tabbatar da cewa, kasar Sin ita ce aminiyar Afirka ta gaskiya.

A yayin da yake zantawa da wakilin babban rukunin rediyo da talabijin na kasar Sin, Ehizuelen ya bayyana cewa, a yayin ziyarar da suke yi a kasashen Afirka, ministocin harkokin wajen kasar Sin da suka gada a jere, sun jaddada muhimman batutuwa guda uku, wato "kawar da mulkin mallaka", "hadin gwiwa irin na samun nasara tare" da "ci gaban Afirka".

Ehizuelen ya kuma ce, ziyarar ta Wang Yi, za ta kara sa kaimi ga bunkasuwar shawarar "Ziri daya da hanya daya" yadda ya kamata, da gina shawarar a matsayin hanyar hadin gwiwa don fuskantar kalubale, kuma hanyar kiyaye lafiyar jama'a da hanyar farfadowar tattalin arziki da zamantakewa, kuma hanyar samun ci gaba da za ta taimaka wa kasashen Afirka da Sin wajen fitar da damar samun ci gaba. (Mai fassara: Bilkisu)