logo

HAUSA

VOA: 'Yan Afirka na mayar da kasar Sin a matsayin kyakkyawar abokiyar hadin kai

2022-01-11 11:29:22 cri

VOA: 'Yan Afirka na mayar da kasar Sin a matsayin kyakkyawar abokiyar hadin kai_fororder_Nairobi

Shafin yanar gizo na kafar VOA ta Amurka, ya ruwaito a baya-bayan nan cewa, kasar Sin na kyautata halin da Kenya da sauran kasashen Afirka suke ciki, ta hanyar raya ayyukan more rayuwa da zuba jari. 'Yan Afirka galibinsu suna da kyakkyawan ra'ayi game da kasar Sin.

Wani binciken da kungiyar Afrobarometer ta gudanar a tsakanin shekarar 2019 da ta 2020 a kasashen Afirka 34, ya nuna cewa kashi 63 cikin 100 na 'yan Afirka sun yi imanin cewa, kasar Sin ta kawo wa nahiyar Afirka kyakkyawan tasiri daga waje.

A watan da ya gabata, lokacin da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya duba wata hanyar mota ta zamani dake Nairobi, wadda wani kamfani na kasar Sin ya shimfida, ya ce, dangantakar da ke tsakanin kasarta da kasar Sin, irin dangantakar hadin gwiwa ce ta cimma moriyar juna bisa samun nasara tare. Ya ce kokarin kyautata ababen more rayuwa zai kara samar da sauki ga zaman rayuwar jama’a, yana kuma taka muhimmiyar rawa ga bunkasar tattalin arzikin kasarsa ta Kenya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)