logo

HAUSA

Mataimakin firaministan Sin ya jaddada bukatar karfafa nasarorin da aka cimma wajen yakar fatara

2022-01-10 10:50:47 CRI

Mataimakin firaministan kasar Sin Hu Chunhua, ya jaddada muhimmancin karfafa nasarorin da aka samu wajen kawar da fatara, yana mai kira da a yi kokarin kare al’ummun karkara daga kara fadawa cikin kangin talauci, kana a inganta ci gaban yankunan da suka fattaki talaucin.

Hu ya yi wannan tsokaci ne lokacin da ke rangadi a yankin Guangxi Zhuang mai cin gashin kansa, dake kudancin kasar Sin, daga ranar 6 zuwa 9 ga wata.

Mataimakin firaministan ya ziyarci yankunan masana’antu da kamfanoni da wuraren da aka sake tsugunar da jama’a da gidajen mazauna karkara a wasu muhimman yankunan, yana mai nanata bukatar taimakawa irin wadannan yankunan inganta karfinsu na raya kansu. (Fa’iza Mustapha)