logo

HAUSA

Za a bude makarantu a Uganda daga ranar Litinin din nan

2022-01-10 10:32:02 CRI

Za a bude makarantu a Uganda daga ranar Litinin din nan_fororder_220110-Saminu2-Uganda

Iyayen yara a Uganda, na ta shirye shiryen maida yaran su makarantu tun daga Litinin din nan 10 ga watan Janairu, bayan da aka rufe makarantun kasar tsawon lokaci sakamakon bazuwar cutar COVID-19. 

Ministar ilimi da wasanni ta kasar Janet Kataaha Museveni, ta ce gwamnati ta amince da sake bude makarantun renon yara, da na firamare, da kuma na sakandare tun daga yau Litinin.

Wata ’yar kasuwa da ta zanta ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Xinhua Brenda Kizito ta ce, a yanzu haka kasuwa ta bude a birnin Kampala, sakamakon sayayya da iyayen yara ke yiwa ’ya’yan su, gabanin komawa makaranta. Kizito ta kara da cewa, cikin makwanni 2 da suka gabata, yawan masu sayayya ya ninka sama da rubi 2.

Rahotanni sun bayyana cewa, makarantu sun sanya sinadarin kashe kwayoyin cuta, da murfin baki da hanci, da sabulu cikin abubuwan da suka wajaba dalibai su mallaka, yayin da suke komawa makaranta, a wani mataki na dakile sake bullar annobar COVID-19. (Saminu Hassan)