logo

HAUSA

Wang Qishan ya halarci taron tattaunawa na biyu kan musayar ra'ayi da fahimtar juna tsakanin al'ummomi

2022-01-10 20:30:06 CRI

Litinin din nan ne, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo a yayin taron tattaunawa karo na 2, kan musaya da fahimtar juna tsakanin al'ummomi.

Yayin jawabin nasa, Wang Qishan ya jaddada cewa, kokarin yin mu'amala da fahimtar juna a tsakanin al'ummomi daban-daban, wani batu ne mai muhimmanci game da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya, da ma rayuwar jama'a. Ya ce, JKS ta yi nasarar jagorantar jama'ar kasar Sin wajen kiyayewa da raya tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin, da samar da wani sabon salo na wayewar kan dan Adam.

Wang Qishan ya ce, tabbatar da tsarin demokuradiyya da 'yanci, manufa ce ta dukkan bil'Adama, kuma ba za a iya auna wayewar siyasar duniya da ma'auni guda ba. Jami’in na kasar Sin ya ce, a shirye muke mu yi aiki tare da kowane bangare don mutuntawa, da amincewa da koyi da juna, da kuma gano sabbin hanyoyin ci gaba, da ma ci gaban tafarkin demokuradiyyar dan Adam.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya