logo

HAUSA

Kasar Sin ta kara daukar matakan dakile abubuwa masu illa wadanda ba bisa ka'ida ba

2022-01-10 20:26:03 CRI

Alkaluman hukuma na nuna cewa, kasar Sin ta gudanar da bincike tare da gudanar da shari'o'i sama da 13,000 da suka shafi abubuwan da aka aika ta intanet da na zahiri da wallafe-wallafe da suka saba doka a cikin shekarar 2021.

Ofishin yaki da ayyukan batsa da wallafe-wallafe da suka saba doka na kasar Sin ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, hukumomi a fadin kasar Sin, sun kwace wasu bayanai da aka wallafa kusan miliyan 15 da suka saba ka'ida, wadanda suka hada da haramtattun litattafai miliyan 3.8, da wallafe-wallafe masu cutarwa ga yara da littattafai da suka sabawa ‘yancin mallakar fasaha da kuma littattafan bincike.

Ofishin ya kara da cewa, a halin da ake ciki, an goge kusan abubuwa miliyan 19 na bayanai masu cutarwa da ke dauke da abubuwan batsa ko na lalata

Ofishin ya ce, hukumomin kasar Sin sun kuma rufe shafukan yanar gizo da suka sabawa doka, fiye da 110,000 a wani kamfel da mahukuntan kasar ka yi kan tsaftace harkar Intanet a shekarar 2021. Gangamin yana kokarin mayar da hankalin ne kan bayanai masu cutarwa a wuraren da ake watsa su kai tsaye, da wasannin Intanet da adabi, da shafukan sada zumunta, da tallace-tallace ta shafukan Intanet.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya