logo

HAUSA

Jami’ar Johns Hopkins: Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Amurka ya zarce miliyan 60

2022-01-10 10:42:05 CRI

Jami’ar Johns Hopkins: Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Amurka ya zarce miliyan 60_fororder_病毒

Alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta fitar sun nuna cewa, adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Amurka ya kai miliyan 60 ya zuwa jiya ranar Lahadi.

Kamar yadda alkaluman suka nuna, yawan mutanen da cutar COVID-19 ta kama a Amurka ya kai 60,062,077, yayin da cutar ya kashe Amurkawa  837,504, ya zuwa karfe 4:21 na yammaci, agogon kasar wato karfe 21:21 agogon GMT.

Amurka ce kasar da annobar ta fi yiwa mummunar barna, inda kasar take da adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar da kuma wadanda cutar ta kashe a fadin duniya, wato adadin ya kai kashi 20 bisa 100 na yawan mutanen da suka kamu da cutar, kana sama da kashi 15 bisa 100 na wadanda annobar ta hallaka a duk duniya.(Ahmad)