logo

HAUSA

Sabuwar majalisar dokokin Iraqi ta sake zabar al-Halbousi a matsayin shugabanta

2022-01-10 11:37:02 CRI

Sabuwar majalisar dokokin Iraqi ta sake zabar al-Halbousi a matsayin shugabanta_fororder_220110-Ahmad3-Iraq

A jiya Lahadi sabuwar majalisar dokokin kasar Iraqi ta sake zabar Mohammed al-Halbousi a matsayin shugaban majalisar bayan da majalisar da gudanar da zamanta na farko.

Zaman majalisar wanda Khalid al-Darraji, wato mutumin dake kan matsayi na biyu wajen jagorantar zaman majalisar bayan wani dan majalisar daban, wanda yake kan matsayi na farko wajen shugabantar zaman, ya ki jagorantar zaman majalisar bayan malam Mahmoud al-Mashhadani, wanda aka garzaya da shi zuwa asibiti sakamakon matsalar lafiya ta gaggawa.

Zaman majalisar ya samu mahalarta mambobi 228 daga cikin adadin mambobin majalisar dokokin kasar 329, wadanda suka zabi al-Halbousi ko kuma al-Mashhadani a matsayin kakakin majalisar. (Ahmad Fagam)