logo

HAUSA

ECOWAS ta kakaba takunkumai masu tsauri a kan Mali

2022-01-10 10:13:40 CRI

Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS, sun sanar da kakabawa Mali wasu takunkumai masu tsauri

Shugabannin kungiyar sun gudanar da taro ne jiya a Accran Ghana, domin tattauna yanayin da kasar Mali ke ciki. Cikin wata sanarwar bayan taro, kungiyar ta ce kudurin da gwamnatin riko ta Mali ta gabatar na rike mulki na tsawo shekaru 5 da rabi, ba abu ne mai yiwuwa ba.

Sanarwar ta ce dukkan kasashe mambobin kungiyar za su janye jakadunsu daga Mali.

Sauran takunkuman sun hada da rufe iyakokin kasa da na sama tsakanin Mali da kasashen kungiyar, da dakatar da hada-hadar kudi da na tattalin arziki tsakaninsu da Mali, in banda na muhimman kayayyakin bukatun jama’a.

Takunkuman ba su shafi batun samar da magunguna da kayayyakin lafiya ba, ciki har da kayayyakin dakile COVID-19 da albarkatun man fetur da lantarki.  (Fa’iza Mustapha)