logo

HAUSA

Ya Kamata A Saurari Yadda Wadanda Suka Ziyarci Xinjiang Suka Fada Game Da Jihar

2022-01-09 16:56:20 CRI

Ya Kamata A Saurari Yadda Wadanda Suka Ziyarci Xinjiang Suka Fada Game Da Jihar_fororder_0109-1

Kamfanin Tesla na kasar Amurka ya bayar da labari a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2021 cewa, an bude cibiyar Tesla ta birnin Urumqi a hukumance, wadda ta kasance cibiyar Tesla ta farko da aka bude a jihar Xinjiang. Amma wasu ‘yan siyasar kasar Amurka sun zargi wannan batu. Ra’ayoyinsu suna da nasaba da batun kafa daftarin dokar kasar Amurka na hana tilastawa ‘yan Uygur yin aiki, wasu ‘yan siyasar kasar Amurka suna neman yin amfani da daftarin dokar don hana kamfanonin kasar Amurka su yi ciniki ko yin mu’amala tare da jihar Xinjiang ta kasar Sin. Amma aikin kamfanin Tesla bai bi ra’ayin ‘yan siyasar ba.

Mene ne hakikanin yanayin jihar Xinjiang? Kamfanin Tesla ya amsa wannan tambaya ta hanyar bude cibiyarsa a jihar, kana sauran mutanen kasashen waje su ma sun amsa wannan tambaya ta hanyar ziyararsu a jihar Xinjiang.

A shekaru fiye da 30 da suka gabata, wani gidan telebijin na kasar Japan ya dauki wani bidiyo game da hanyar siliki, wanda ya janyo hankalin jama’ar kasar Japan sosai. Kafofin watsa labaru na kasar Japan da dama sun tura wakilansu zuwa kasar Sin don tattara labaru, da kuma jama’ar kasar Japan da dama sun ziyarci kasar Sin don yin yawon shakatawa.

Ya Kamata A Saurari Yadda Wadanda Suka Ziyarci Xinjiang Suka Fada Game Da Jihar_fororder_0109-2

Ban da mutanen kasar Japan, akwai mutane daga sauran kasashen duniya da suka ziyarci kasar Sin da kuma ziyartar jihar Xinjiang. A cikinsu, Raz Galor daga kasar Isra’ila ya fi janyo hankalin kasa da kasa, wanda yake da masu bin shafinsa fiye da miliyan 30 a shafin sada zumunta na yanar gizo. Lokacin da ya ziyarci jihar Xinjiang a shekarar 2021, ya gamu da wani tsoho mai shuka auduga a jihar Xinjiang. Ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani na shuka auduga, wannan tsoho yana iya samun kudin shiga Yuan dubu 700 zuwa 800 a kowace shekara. A ganin Raz Galor, mazaunen jihar Xinjiang suna da ikon yin magana kan zaman rayuwarsu.

A shekarar 2020, yawan masu yawon shakatawa da suka ziyarci jihar Xinjiang ya kai miliyan 158, wadanda suka gano bunkasuwar jihar ta Xinjiang tare da daukar hotuna ko bidiyo kan yanayin jihar da kansu.

Wadancan ‘yan siyasa na kasar Amurka ba su taba ziyartar jihar Xinjiang ba, ra’ayoyinsu kan jihar ba su da tushe ko kadan. (Zainab)