logo

HAUSA

‘Yan fashin daji sun kashe a kalla mutane 58 a hare-hare a arewa maso yammacin Najeriya

2022-01-09 16:14:16 CRI

A kalla mutane 58 ‘yan fashin daji suka kashe a hare-haren da suka kai wasu kauyuka a kananan hukumomi biyu na jahar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.

Ibrahim Bello Zauma, kakakin gwamnan jahar Zamfara Bello Matawalle, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yayin zantawa ta wayar tarho cewa, hare-haren sun faru ne a ranakun Laraba da Alhamis a kauyuka da dama dake kananan hukumomin Anka da Bukkuyum dake jahar.

Zauma ya kara da cewa, kawo yanzu, an samu hasarar rayukan mutane 36 a karamar hukumar Bukkuyum, da kuma mutuwar wasu 22 a karamar hukumar Anka.

Ya ci gaba da cewa, gwamnan jahar ya ziyarci yankunan da lamarin ya faru domin yin ta’aziyya ga mutanen yankunan sakamakon hare-haren da ‘yan fashin dajin suka kaddamar a yankunan.

A cewar kafafen yada labaran wurin, kimanin kauyuka hudu aka cinnawa wuta a hare-haren wanda aka fara a ranar Laraba. Kuma jami’an tsaron sa kai na bijilanti wadanda suka yi kokarin dakile hare-haren na daga cikin wadanda aka kashe a hare-haren.

Zauma ya nuna cewa, gwamnatin jahar tana ci gaba da aiwatar da dabarun kawo karshen hare-haren ‘yan bindigar a jahar.(Ahmad)

Ahmad