logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwaransa na kasar Comoros

2022-01-08 16:17:11 cri

Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwaransa na kasar Comoros_fororder_W020220107790557775129

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Comoros Dhoihir Dhoulkamal, jiya Jumma’a a birnin Moroni.

A yayin ganawar, Dhoihir Dhoulkamal ya bayyana cewa, ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai kasarsa a farkon sabuwar shekara, wata alama ce ta 'yan uwantaka da kyakkyawan hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. Ya ce a ko da yaushe, kasarsa ta kasance mai bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma ba za ta canja matsayinta ba. Har ila yau, ya ce kasar tana son hada hannu da kasar Sin, don kai hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban zuwa wani sabon matsayi.

Baya ga haka, ya kara da cewa, shawarar da kasar Sin ta sanar yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, ta karawa kasashen Afirka kwarin gwiwa sosai. A cewarsa, taron ya samar da kyakkyawan dandali ga bangarorin biyu, wajen zurfafa dangantakar abota da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, tare da ba da taimako ga Comoros wajen ciyar da shirinta na raya kasa nan da shekarar 2030.

A nasa bangaren, Wang Yi ya ce, yayin da ake fuskantar kalubalen annobar COVID-19, kasar Sin ta samar da alluran rigakafi da kayayyakin yaki da cutar ga kasar Comoros cikin gaggawa, ta kuma aike da tawagar likitoci zuwa kasar, kana kuma bisa bukatar Comoros din, kasar Sin za ta ci gaba da samar da alluran rigakafin da na'urorin gwaji, domin taimakawa kasar cimma burinta na yi wa dukkan al’ummarta riga kafi.

Haka zalika, ya ce kasar Sin tana son sa kaimi ga aiwatar da "ayyuka tara" na hadin gwiwar Sin da Afirka a Comoros, don hada su da shirin raya kasar nan da shekarar 2030, lamarin da zai taimaka mata wajen samun gagarumin ci gaba. Ban da wannan kuma, Wang Yi ya yi maraba da Comoros ta yi amfani da hanyar samar da sauki ta fitar da kayayyakin amfanin gona na Afirka zuwa kasar Sin, da kuma manufar rashin biyan harajin kayayyakin da ake samu daga kasashe mafi karancin ci gaba zuwa kasar Sin, ta yadda za a kara tallatawa da shigar da kayayyaki masu inganci daga kasar ta Comoros zuwa kasuwar kasar Sin. (Mai fassara: Bilkisu)