logo

HAUSA

Shugaban Nijeriya ya tabbatar da mutuwar fasinjoji 19 sanadiyyar hatsarin mota a kasar

2022-01-08 15:45:59 CRI

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya tabbatar a jiya Juma’a cewa, wasu fasinjoji 19 sun rasa rayukansu yayin wani hatsarin mota da ya auku a yankin arewa maso yammacin kasar a ranar Alhamis.

Cikin wata sanarwa, shugaba Buhari ya bayyana hatsarin da ya auku a kan hanyar Kano zuwa Zaria a matsayin abin tausayi, yana mai jimamin asarar rayukan da aka yi.

A cewar kafafen yada labarai na kasar, fasinjoji 26 sun jikkata yayin hatsarin da ya auku sanadiyyar arangamar da wasu motocin bas biyu suka yi, inda nan take wuta ta tashi, lamarin da ya kai ga konewar fasinjoji da dama.

A cewar shugaban, ya fahimci cewa gudun wuce kima ne ya haifar da hatsarin, lamarin da ya ce abun damuwa ne a gareshi, yana mai takaici yawan hatsurran mota dake aukuwa, inda ya yi kira da a kara mayar da hankali kan muhimmanci ka’idojin hanya.

Ya kuma shawarci direbobi da su rika daukar matakan kariya da muhimmanci, yana mai cewa hakkinsu ne tabbatar da kare fasinjoji. (Fa’iza Mustapha)