logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci Amurka ta daina amfani da demokuradiyya a matsayin wata hanya ta shirya makarkashiya

2022-01-08 16:14:22 CRI

Kasar Sin ta bukaci Amurka ta daina amfani da demokuradiyya a matsayin wata hanya ta shirya makarkashiya_fororder_cb8065380cd791239e763addbbeee98bb0b780ec

Kasar Sin na fatan Amurka, za ta daina amfani da demokuradiyya a matsayin wata hanya ta kulla makarkashiyar siyasa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na jiya, inda aka nemi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka game na cika shekara guda da gudanar da zanga-zangar ginin Capitol na kasar, inda ya ce “daga Sin zuwa Rasha da sauransu, suna ganin kamar demokradiyya na gab da karewa, amma ban yarda da hakan ba”

A cewar Wang Wenbin, demokradiyya abu ne mai daraja ga daukacin bil adama da ba za ta taba karewa ba.

Ya ce a daya bangaren, kakaba salon demokuradiyyar wata kasa a kan wata, da fito na fito da ingiza rarrabuwar kawuna, wadda demokradiyya ce ta bogi da ta sabawa ruhin ainihin demokradiyya, ita ce ke gab da zuwa karshe, wadda kuma za ta fuskanci turjiya daga al’ummun duniya. (Fa’iza Mustapha)