logo

HAUSA

Xi ya aike da sakon jaje ga shugaban Mauritania

2022-01-08 15:53:25 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon jaje a yau Asabar, ga takwaransa na kasar Mauritania Mohamed Ould Ghazouani, bisa kamuwa da ya yi da cutar COVID-19.

Cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce ya samu labarin kamuwa da cutar da shugaba Ghazouani ya yi, a don haka yake jajanta masa tare da yi masa fatan samun lafiya da wuri.

A cewarsa, gwamnati da al’ummar Sinawa, na goyon bayan takwarorinsu na Mauritania wajen yaki da annobar COVID-19, yana mai cewa, ya yi ammana karkashin shugabancin Ghazouani, Mauritania za ta ci galaba kan annobar nan bada jimawa ba. (Fa’iza Mustapha)