logo

HAUSA

WHO: Kamfanonin Sinopharm da Sinovac muhimman ginshikai ne ga shirin COVAX

2022-01-07 10:23:04 CRI

WHO: Kamfanonin Sinopharm da Sinovac muhimman ginshikai ne ga shirin COVAX_fororder_220107-A2-whoallura

Wani babban jami’in hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce, sama da alluran riga-kafin COVID-19 miliyan 180 kamfanonin Sinopharm da Sinovac suka aikewa kasashe 49 karkashin shirin COVAX, inda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen karfafa garkuwar jiki da kuma ceto rayuwar al’umma.

Bruce Aylward, babban mashawarci ga darakta janar na hukumar WHO, ya ce riga-kafin biyu na kasar Sin sun samar da kusan kashi 20 bisa 100 na jimillar adadin riga-kafin da aka samar ga shirin COVAX, wato shirin rarraba alluran riga-kafin COVID-19 na kasa da kasa wanda hukumar WHO ke jagoranta.

Bugu da kari a ranar Alhamis, babban daraktan sashen ayyukan lafiyar gaggawa na hukumar WHO, Mike Ryan ya ce, babu karin barazanar yaduwar COVID-19 ga wasannin Olympic na lokacin hunturu na Beijing dake tafe, kasancewar hukumomin kasar Sin suna daukar tsauraran matakai masu karfi wajen dakile yaduwar annobar. (Ahmad Fagam)