logo

HAUSA

Minista: Kamaru ta kammala shirin karbar bakuncin gasar kofin Afrika

2022-01-07 11:40:17 CRI

Minista: Kamaru ta kammala shirin karbar bakuncin gasar kofin Afrika_fororder_220107-A4-Kamaru

Ministan wasannin jamhuriyar Kamaru, Narcisse Mouelle Kombi, ya sanar cewa kasarsa ta kammala dukkan shirye shiryen karbar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika ta (AFCON).

Kasar Kamaru ta sha fuskantar matsin lamba game da shirinta na karbar bakuncin gasar wasannin sakamakon rashin kammala aikin katafaren filin wasan na Olembe dake kasar wanda aka tsara za a bude wasannin da kuma rufewa a cikinsa.

Kombi ya ce, an kammala muhimman ayyukan shirya filin wasan, kuma filin ya shirya karbar bakuncin kasaitaccen bikin bude gasar wasannin.

Sama da kungiyoyin wasannin kasashen Afrika 10 sun riga sun isa kasar ta tsakiyar Afrika domin halartar gasar wasannin mafi girma ta Afrika.

Kungiyoyin wasannin 24 ne zasu fafata a wasannin, wanda za a bude a ranar Lahadi, inda Kamaru mai masaukin baki zaka fafata da Burkina Faso a filin wasan na Olembe mai kujeru 60,000 dake Yaounde babban birnin kasar.

Ana sa ran kammala gasar ta wannan karo wacce ake gudanarwa duk bayan shekaru biyu a ranar 6 ga watan Fabrairu. (Ahmad Fagam)