logo

HAUSA

Kwarewar kasar Sin a fannin kirkiro sabbin fasahohi ta kai matsayi na 12 a duniya

2022-01-07 10:54:25 CMG

A jiya Alhamis, an kira taron ayyukan kimiya da fasaha na kasar Sin na shekarar 2022, inda aka takaita nasarorin da aka samu a shekarar 2021, gami da tsara manyan ayyukan da za a gudanar a bana.

An bayyana a wajen taron cewa, kwarewar kasar Sin a fannin kirkiro sabbin fasahohi ta hau matsayi na 12 a duniya. Kana nasarorin da kasar ta cimma a fannin kimiyya da fasaha a bara sun hada da hada garin sitati a cikin dakin gwaji wanda ya kasance karo na farko a duniya, da harba na’urar binciken duniyar Mars, da ta binciken rana, da yadda aka samu nasarar hada kumbon Shenzhou-13 da wani bangaren tashar bincike a sararin samaniya, da saukar da na’urar bincike zuwa wani wuri mai matukar zurfi a cikin teku, lamarin da ya karya matsayin bajinta a duniya.

An ce nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da kokarin raya bangaren kimiyya da fasaha, da gudanar da karin hadin gwiwa tare da sassan duniya, da shiga a dama da ita a kokarin kula da ayyuka masu alaka da kimiyya da fasaha na duniyarmu. (Bello Wang)

Bello