logo

HAUSA

Lianhe Zaobao: Sin tana da kwarin gwiwa da kuma karfin karbar bakuncin gasar wasannin Olympic

2022-01-07 16:17:21 CRI

Lianhe Zaobao: Sin tana da kwarin gwiwa da kuma karfin karbar bakuncin gasar wasannin Olympic_fororder_220107-推送-Beijing Olympics

Jaridar “Lianhe Zaobao” ta kasar Singapore, ta bada rahoto a ranar 5 ga watan Janairu cewa tsarin kandagarki da kuma dakile yaduwar annobar na cikin gida, da yin riga-kafi, da sanya ido ga masu shigowa cikin kasa, da tsarin gudanar da aiki bisa dacewa, da kokarin kare kai da sauran matakan yaki da annobar a lokacin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, duka an yi cikakken gwajinsu a lokacin gudanar da gasar gwaji. Cimma nasarar karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin hunturu da ta nakasassu na Beijing wani alkawari ne da kasar Sin ta daukawa al’ummun kasa da kasa. Kasar Sin tana da cikakkiyar kwarin gwiwa da kuma burin taimakawa ci gaban duniya, da kyakkyawan shirin karbar bakuncin gasar wasnnin Olympic ta lokacin hunturu. (Ahmad Fagam)