logo

HAUSA

Zhang Yimou ne zai jagoranci bikin bude gasar Olympics ta birnin Beijing dake karatowa

2022-01-07 20:36:57 CRI

Zhang Yimou ne zai jagoranci bikin bude gasar Olympics ta birnin Beijing dake karatowa_fororder_微信图片_20220107203632

An bayyana sunan Zhang Yimou mai shekaru 71 da haihuwa, a matsayin babban daraktan bikin bude gasar wasannin Olympics, ta lokacin hunturu ta birnin Beijing dake tafe. Zhang shi ne ya jagoranci kasaitaccen bikin bude da na rufe gasar Olympics ta lokacin zafi a shekarar 2008 a birnin Beijing.

Yayin da ya rage kasa da wata guda a bude wannan babbar gasa, kwamitin shirya gasar ya bayyana mambobin tawagar gudanarwar da bikin bude ta.

Rahotanni sun bayyana cewa, Zhang zai jagoranci tawagar kwararru, wadda za ta tsara gabatar da kasaitaccen bikin bude gasar, wanda za a yi a ranar 4 ga watan Fabarairu dake tafe. Gasar za ta gudana tsakanin ranekun 4 zuwa 20 ga watan na Fabarairu.  (Saminu)