logo

HAUSA

Shugaban kasar Pakistan ya kamu da cutar COVID-19 a karo na biyu

2022-01-07 10:46:26 CRI

Shugaban kasar Pakistan ya kamu da cutar COVID-19 a karo na biyu_fororder_220107-A3-Pakistan

Shugaban kasar Pakistan Arif Alvi, ya kamu da cutar COVID-19 a karo na biyu, shugaban ya wallafa a shafinsa na twita a jiya Alhamis.

A watan Maris na shekarar bara, Alvi ya kamu da cutar kana ya warke bayan ya killace kansa a gida. Sai dai shugaban ba ya cikin yanayi mai tsanani a lokacin da yake jinyar cutar.

Ya umarci al’ummar kasar da su kiyaye dokokin da gwamnati ta kafa don dakile yaduwar annobar ta COVID-19.

Shugaban kasar ya kamu da cutar ne a daidai lokacin da hukumomin lafiyar kasar Pakistan suke gargadin al’ummar kasar game da barkewar cutar COVID-19 a karo na biyar a kasar wanda nau’in Omicron ya haddasa. (Ahmad Fagam)