logo

HAUSA

Birnin Douala ya kafa wuraren zaman masu sha’awar wasanni gabanin gasar AFCON

2022-01-06 11:17:27 CRI

Birnin Douala ya kafa wuraren zaman masu sha’awar wasanni gabanin gasar AFCON_fororder_0106-Kamaru-Faeza

Babban birnin hada-hadar kasuwanci na Kamaru wato Douala, ya kafa wuraren zaman masu sha’awar wasanni a muhimman sassan birnin da zai karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afrika dake karatowa.

Samuel Dieudonne Ivaha Diboua, gwamnan yankin Littoral, da Douala ke zaman babban birninsa, ya ce wuraren za su mayar da hankali ne wajen kula da baki da mazauna birnin a wajen filayen wasa, wato wadanda ba za su iya sayen tikitin shiga ba.

A cewarsa, wannan wata hanya ce dake nuna cewa, birnin Doula ya shirya karbar bakuncin mutane. Ya ce mazauna na alfahari da kuma maraba da jama’a, tare da nuna musu al’adun birnin. Yana mai cewa wuraren za su cika da abubuwan nishadi yayin wasannin na AFCON.

Gwamnan ya bayyana haka ne ga manema labarai a jiya, yayin da yake kaddamar da yankin mai fadin murabba’in mita 400 da zai iya daukar mutane 1,500. Wanda aka katange yake kuma dauke da inuwa daga bishiyoyi.

Baya ga watsa wasannin AFCON kai tsaye a wuraren, jarumai na gida da kasashen waje da masu nune-nune da kide-kide da masu abinci, za su gudanar da shirye-shirye kai tsaye a wuraren. (Fa’iza Mustapha)