logo

HAUSA

Alluran rigakafin Sinopharm, da Sinovac sun magance kwantar da marasa lafiya da suka kamu da Omicron

2022-01-06 10:03:20 CRI

Alluran rigakafin Sinopharm, da Sinovac sun magance kwantar da marasa lafiya da suka kamu da Omicron_fororder_0106-rigakafi-Ibrahim

Kafar yada labarai ta hadaddiyar daular Larabawa (UAE), mai suna The National, ta ruwaito Abdi Mahamud, kwararre a hukumar Lafiya ta duniya (WHO) na cewa, alluran rigakafin COVID-19 na kamfanonin Sinopharm da Sinovac na kasar Sin, suna ba da kariya daga tsananin kwantar da marasa lafiya da nau’in COVID-19 na Omicron ke haifarwa. 

Abdi Mahamud, manajan hukumar ta WHO game da cutar ya ce, karin shaidun na nuna cewa, Omicron yana shafar bangaren sama da mutum ke yin numfashi, lamarin dake haifar da alamu marasa sarkakiya fiye da raguwar nau’o’in cutar da suka gabata.

Rahoton ya ce, a kwanan baya hadaddiyar daular Larabawa (UAE) ta amince da yin amfani na gaggawa, da wani sabon allurar rigakafin da Sinopharm ta samar, a matsayin allurar kara karfin garkuwar jiki a kasar.

A cewar ma’aikatar lafiyar kasar, sabuwar allurar rigakafin ta kasar Sin, ta nuna ingancin rigakafi a kan sabon nau’in cutar, gami da rashin wata illa, matakin da ke ba da damar kara samar da ita cikin sauri da saukin adanawa da kuma rarrabawa. (Ibrahim Yaya)