logo

HAUSA

Sin ta cimma nasarar sauya wurin kumbon jigilar kayayyaki a sararin samaniya

2022-01-06 10:50:28 CRI

Sin ta cimma nasarar sauya wurin kumbon jigilar kayayyaki a sararin samaniya_fororder_1128236200_16414339000061n

Yau Alhamis, da misalin karfe 6 da mintoci 59 na safiya, na’urori daban-daban na tashar sararin samaniya ta kasar Sin suka kwashe mintoci 47 suna hada kansu, inda suka cimma nasarar sauya wurin kumbon jigilar kayayyaki. Wannan shi ne karon farko da Sin ta gudanar da wannan gwaji a sararin samaniya.

Babbar injiniya dake kula da kumbon jigilar kayayyaki ta cibiyar ba da jagoranci ga zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta Beijing Madam Zou Xuemei ta shaidawa manema labarai cewa:

“Na’urorin tashar sararin samaniya ta kasar Sin za su yi aikin gwaji mai wuya nan gaba don hada kumbon gwaji 1 da na 2 tare, wanda ke bukatar kwarewa da fasaha matuka. Abin da muka yi a wannan rana aikin share fage ne ga gwaje-gwajen da za a yi.”

Bisa labarin da aka bayar, na’urar da aka yi amfani da ita a wannan karo nau’ura ce mai kunshe da fasahohin zamani masu sarkakiya, kuma irinta ce mafi girma a cikin tsarin na’urorin zamani na tashar. Wadda kuma ke da tsayin mita 10.2, dake iya daukar kayan da nauyinsa ya kai ton 25. Na’urar na da amfani matuka wajen sauya wurin kumbon gwaji da ba da taimako ga ‘yan saman jannati da za su fita daga tashar. (Amina Xu)