logo

HAUSA

An baiwa 'yan Uganda damar taba kudaden zamantakewa da suka adana saboda COVID-19

2022-01-06 10:40:11 CRI

An baiwa 'yan Uganda damar taba kudaden zamantakewa da suka adana saboda COVID-19_fororder_0106-Uganda-Ibrahim

Mahukuntan Uganda sun baiwa masu matsakaicin shekaru dake fama da yanayin rayuwa a lokacin bala'in COVID-19, damar taba kudaden ajiyar zamantakewa da suka adana.

Ministar jinsi, kwadago da ci gaban zamantakewa ta kasar Uganda Betty Amongi, ta shaida wa manema labarai cewa, duk wanda yake ciki wannan shiri da ya kai shekaru 45 zuwa sama, sannan ya saka kudade a wannan asusu na tsawon a kalla shekaru 10, ya cancanci amfana da fa’idodin ajiyar na tsakiyar wa’adi, na adadin da bai wuce kashi 20 cikin 100 na ribar da ya samu ba.

Ta ce nakasassu, wadanda shekarunsu suka kai 40, kuma sun biya kudin inshora na tsawon shekaru a kalla 10, su ma suna da damar samun kusan kashi 50 cikin 100 na kudaden ajiyarsu.

A shekarar 2020 ne dai majalisar dokokin kasar, ta gabatar da daftarin gyara dokar asusun tsaron jama'a, don taimakawa ma'aikata samun damar taba ajiyar su, don biyan kudaden jinyar COVID-19 da aka yi musu a asibiti. A ranar Lahadin da ta gabata ce kuma, shugaba Yoweri Museveni ya sanya hannu a kan dokar.

A cewar asusun mai kadarorin da darajarsu ta kai kudin kasar shilling tiriliyan 15.6 , kimanin dalar Amurka biliyan 4.5, a kalla mutane 113,000 ne suka cancanci taba kudaden nasu. (Ibrahim Yaya)