logo

HAUSA

Inganta raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” a yammacin Asiya da arewacin Afirka

2022-01-06 21:26:48 cri

Inganta raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” a yammacin Asiya da arewacin Afirka_fororder_src=http___oeimg2.cache.oeeee.com_202004_25_2501587820712&refer=http___oeimg2.cache.oeeee

Jiya Laraba, gwamnatocin kasashen Sin da Morocco sun rattaba hannu kan shirin hadin gwiwa game da raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”.

Game da haka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana a yayin manema labaru da aka saba yi a yau, cewa kasarsa na fatan amfani da wannan dama mai kyau, don inganta raya shawarar din sosai yadda ya kamata a yankunan dake yammacin Asiya da arewacin Afirka.

Wang ya kara da cewa, Morocco ita ce kasa ta farko a arewacin Afirka da ta rattaba hannu kan shirin hadin gwiwa don gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” tare da kasar Sin. (Bilkisu Xin)