logo

HAUSA

Masanin Mali: Jawabin shugaba Xi na murnar shiga sabuwar shekara ya bayyana kulawarsa ga daukacin al’ummar duniya

2022-01-05 20:40:08 CRI

Masanin Mali: Jawabin shugaba Xi na murnar shiga sabuwar shekara ya bayyana kulawarsa ga daukacin al’ummar duniya_fororder_A

Masanin harkokin kasa da kasa daga kasar Mali, wanda kuma shi ne darektan sashin nazarin kasashe masu magana da harshen Faransanci, a cibiyar nazarin Afirka dake jami’ar horas da malamai a lardin Zhejiang na kasar Sin, Mista Yoro Diallo ya bayyana cewa, jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar na murnar shiga sabuwar shekara ta 2022, ya bayyana kulawarsa sosai ga al’umma, gami da duk duniya baki daya.

A jawabin Xi, ya ce “duk ziyarar da na yi a gidajen mutane, na kan tambaya ko sun gamu da wata matsala. Na kan rike kalamansu a zuciya”, “Ni ma na fito daga yankin karkara, na fahimci menene zaman talauci”. Mista Diallo ya ce furucin shugaba Xi, na sa a kara fahimtar babban burin da jam’iyyar kwaminis, gami da gwamnatin kasar Sin ke neman cimmawa, wato biyan bukatun al’umma na neman jin dadi, kuma wannan shi ne babban dalilin da ya sa jam’iyyar kwaminis, gami da gwamnatin Sin suka iya samun goyon-baya daga wajen al’umma.

Mista Diallo ya kara da cewa, jawabin Xi, ya kara bayyana yadda yake lura da dukkanin duniya, da goyon-bayan kasar Sin kan ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban, da yadda kasar ke aiwatar da ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)