logo

HAUSA

Wang Wenbin: Ya kamata Lithuania ta gyara kurakuran ta yadda ya kamata

2022-01-05 20:13:07 CRI

Wang Wenbin: Ya kamata Lithuania ta gyara kurakuran ta yadda ya kamata_fororder_faf2b2119313b07e75242fc7a28f3e2a95dd8cc2

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce abu ne mai kyau, ganin yadda kasar Lithuania ta gane kuskuren da ta aikata, amma abu mafi muhimmanci shi ne kasar ta yi gyara na zahiri, ta kuma komawa hanyar gaskiya, ta goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Wang Wenbin, ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai da ya gudana, lokacin da yake tsokaci game da rahotanni dake cewa, shugaban kasar Lithuania Gitanas Nauseda, ya amince da kuskuren da kasar sa ta tafka, game da baiwa mahukuntan yankin Taiwan damar bude ofishin wakilci a kasar sa.

Wang ya ce matakin mahukuntan Lithuania, ya lahanta kyakkyawar alakar dake tsakanin kasar da Sin, kuma amincewa da kuskure da mahukuntan Lithuania suka yi kadai, ba zai warware matsalar da ake ciki ba, ba kuma zai farfado da dangantakar sassan biyu ba. (Saminu)