logo

HAUSA

An Kaddamar Da Cibiyar Watsa Labarai Ta Gasar Wasannin Olympic Ta Lokacin Hunturu Ta Beijing

2022-01-05 15:13:58 CRI

An Kaddamar Da Cibiyar Watsa Labarai Ta Gasar Wasannin Olympic Ta Lokacin Hunturu Ta Beijing_fororder_1

Yau da misalin karfe 10 na safe ne, aka gudanar da taron manema labarai na kaddamar da kakakin kwamitin shirya gasar da cibiyar watsa labarai ta gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing a hedkwatar kwamitin shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing. Kakakin kwamitin Mr. Zhao Weidong da Madam Yan Jiarong sun gana da manema labarai. Yayin gasar, kakakin kwamitin gasar Olympic da na nagasassu ta kasa da kasa wato IOC da IPC, za su jagoranci tarukan manema labarai na wadannan gasanni biyu tare da yin bayanai kan gasanni da dumi-duminsu tare da amsa tambayoyin manema labarai na gida da waje.

A yayin taron, Mr. Zhao Weidong da Madam Yan Jiarong sun gayyaci manema labarai na gida da na waje da su yada labarun gasar, suna kuma sa ran yin hadin gwiwa tare da su a yayin gasar da za a shirya, da yayata ruhin Olympic don taka rawa wajen yakar cutar COVID-19, ta gudanar da wannan gasa cikin nasara. (Amina Xu)