logo

HAUSA

An fara sayar da tikitin gasar cin kofin kasashen Afrika

2022-01-05 10:46:04 CRI

An fara sayar da tikitin gasar cin kofin kasashen Afrika_fororder_220105-ahmad-Afirca Cup

Ranar Talata aka fara sayar da tikicin gasar cin kofin kasashen Afrika na 2022 a Kamaru a hukumance.

Ministan al’amurran wasanni na jamhuriyar Kamaru, Narcisse Mouelle Kombi, wanda kuma shine shugaban kwamitin shirya gasar wasannin, ya bayyana cewa, za a sayar da tikitin ne ta hanyar intanet da kuma wasu shagunan musamman da aka kafa a duk fadin kasar.

Eric Binfon, ministan wasannin motsa jikin kasar ya bayyanawa ’yan jaridu cewa, sun dauki kwararan matakai don kaucewa yin fasa-kwauri. Ya ce sun lura cewa, filin wasansu yana da takaitattun adadin mutanen da zai iya dauka. Don haka abin da suka tsara shi ne ’yan kasar Kamarun da suka fara zuwa ne kadai za su iya samun damar shiga filin wasan.

A cewar Binfon, za a sayar da tikitin ne tsakanin kudin kasar XAF 3,000 da XAF 20,000 (kwatankwacin dala 5 zuwa dala 35) ya danganta da nau’in wajen zaman da kuma rukunin wasannin da za a buga.

Gasar, wadda za ta samu halartar tawagogin ’yan wasa 24, za a bude a ranar Lahadi inda jamhuriyar Kamaru mai masaukin baki za ta fafata da Burkina Faso a filin wasan Olembe mai fadin mita 60,000 dake Yaounde, babban birnin kasar. (Ahmad Fagam)