logo

HAUSA

Kasashe 5 sun fara aiki a matsayin zababbun mambobin kwamitin sulhu na MDD

2022-01-05 10:07:02 CRI

Kasashe 5 sun fara aiki a matsayin zababbun mambobin kwamitin sulhu na MDD_fororder_220105-yaya-UN

Jiya ne kasashen Albania, da Brazil, da Gabon, da Ghana da kuma hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) suka fara aiki a matsayin mambobin da ba na dindindin ba a kwamitin sulhu na MDD.

Ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2022 ne, wa'adinsu na shekaru biyu ya fara aiki a hukumance. Amma jiya Talata, ita ce ranar farko ta fara aiki na majalisar na 2022, bayan dawowa daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

An gudanar da bikin daga tuta domin fara gudanar da ayyukansu.

Wakilan dindindin na sabbin mambobin majalisar biyar sun yi takaitattun jawabai kafin su sanya tutocin kasashensu a wajen zauren majalisar.

Kasashen biyar sun maye gurbin kasashen Estonia, da Jamhuriyar Nijar, da Saint Vincent da Grenadines, daTunisia, da kasar Vietnam. (Ibrahim Yaya)